85

5.2K 297 0
                                    

85

Yau bayan Anty Zuwairah tagama shirinta tsaf tashiga dukkan d'akunan matan gidan, tamusu sallam dasake neman gafararsu, musammam akan abinda taitamusu abaya narashin girmamawa, hakama tanemi gafarar gwaggo bintu akan k'untata rayuwarta dasukayi sanda ta zauna a Lagos, gwaggo bintu tace babu komai yawuce aii, kuma tayafe mata.
      Hakama d'akunan matansu Ramadan Duk saida tashiga tamusu sallama, sannan tashiga mota hafeez da Muhseen sukatafi kaita airport.
        Anty shukurah ma tanufi gidanta, dansuma sundawo nan Nigeria baki d'aya.

_____________________
     Dayake yau takasance asabar kowa yana gida babu aiki.
       Aysha dataji d'an k'arfi-k'arfin jikinta tatashi tunda safe tahau gyaran gidan, khaleel kam Na d'akinsa kwance yana shak'ar barcinsa.
   Bayan tagama tsaftace ko'ina dukda tagaji sosai haka tadaure tashiga kichin, duk tanayine domin faranta ran ya khaleel, aganinta itama yakamata yanzu ta maida hankalinta sosai wajen kulawa da mijinta kamar kowacce mace, burinta yacika akan mafi yawan tanadinta, to shima yakama ta fuskanceshi, Abu mai sauk'i ta shirya amma masu dad'i, bakuma tayi masu yawaba yanda zai zama almabazzaranci da abinci, dai-dai cikinsu tayi, sai kad'an data k'ara koda wani yashigo, dukda haryanzu takanyi amai idan abinci baimataba.
      Bayan tagama wanke kayan data 6ata tafara sharan kicin d'in, jiri takeji kad'an-kad'an amma haka taita dafe bango tana morphing, wani yuuuu dataji acikin kanta yasaka saurin zama akaujerar plastic dake kichind'in, tadafe kanta tana sauke numfashi.
        Ya khaleel datun d'azun ke tsaye yana kallonta ya jinjina kansa yana guntun murmushi, aransa yace agaida jaruma.
     Takowa yayi ahankali har inda take, ya durk'usa agabanta tareda d'ora hannayensa bisa guywoyinta, d'ago ido tayi ahankali tasauk'esu akansa. Ya d'age gira d'aya yana kallonta shima, da hannu yamata alamar mike faruwa?.
    Kanta ta girgiza masa tana murmushi.
    Yace.
"banason k'aryafa".
       Murmushi tayi, tace, " jirine kawai, kuma nadainaji".
       ''Yanzu nan waya sakaki duk wannan aikin? ana lalla6a d'an cikin kekuma kina gingimo masa wahala".
        "Sadauki kenan, idanfa zan biye tawani lalla6awa babu abinda zanma kaina, insha ALLAH ma sonake wannan week d'in dazamu shiga nakoma aikina".
       " yayi k'yau babie". 'Ya khaleel yafad'a yana mik'ewa, morper d'in data ajiye yad'auka yak'arasa morphing d'in kicind'in, itakam sai binsa da kallo takeyi da mamakinsa.
       Bayan ya kammala yace, " oya tashi muje muyi wanka, yau zuminci zamuje".
       "Zumunci kuma sadauki? Ina da ina zamuje?".
       juyowa yayi yana kallonta, ya kashe mata ido d'aya, "to ganin babe zamuje, matar Joseph ta haihu baby boy".
     " woow! Sadauki da gaske Dan ALLAH".
     "I'm telling you my Angel".
     Cikin farin ciki Aysha ta rungumesa, kaikace itace ta haihun, sai gero addu'ar fatan alakairi takeyi akan jaririn.
          Cikin amsawa da ameen ya d'auketa cak, bai direta ako inaba sai toilet.

Nidai najawo tsumman k'afata nadawo falo.
🚶🏻‍♀

Ganin sunk'i fitowa nad'an kwanta jiransu, 'Yar wayata nad'auka nabud'e data, banzame ko ina sai group d'in ciki da gaskiya fans daketa suburbud'a firarsu ya khaleel, can nahango 'yan BBC hausama, suma nad'an lek'a muka gaisa, pherty novels ma hirar suke, dansuma akwai k'ok'arin comments, nashagala sosai a charts najiyo dariya khaleel cikeda nutsuwa.
    Tashi nayi zaune nad'auk'i d'an takardana da alk'alami nacigaba daga Inda Na tsaya😉👍🏻😂.

       Cikin shagwa6a Aysha kefad'in "nidai kakema dariya ko? Babu komai zan ramane aii, kuma saina had'aka da Ammah jar wuya".
     Dariya yakuma tuntsirewa dashi, yamatso kusada Aysha, ''kinga sorry my Angel d'ina, aii had'ani da Ammah tamkar taro March ne."
      ''Kadai gaya musu saina fad'a d'in".
      "OK OK naji, fad'i mikikeso amatsayin cin hanci?".
       " la ila sadauki! Kaima kana karya doka?".
           Cikin d'age gira yace, ''aii kezan bama cin hancin bawaniba, yanzu dai zan saya miki ice-cream, saikuma mi bayanshi".
           "Dan ALLAH da gaske?".
       " eh mana, amma saimun dawo daga ganin baby".
     "Shikenan muje to muyi break fast".
     Break fast suka zaunayi, adaddafe dai aka gama, Dan anyi nisa dacin abincin zuciyar Aysha tafara tashi.
    Cikeda kulawa khaleel yake kallonta, yace, "lafiya kuwa?".
       'Dan yatsine fuska tayi, da hannu tamasa nun amai.
     Tausayi tabashi, yasan tanason abincin wani lokacin, amma data faraci sai labarin ya canja. jikinsa ya zawota, ahankali yayta shafa bayanta, lokaci-lokaci yakan mata sannu.
     Kanta kawai take d'aga masa, talafe ajikinsa tana shak'ar k'amshin turarensa.
      Zuwa wani lokaci yad'agota. Idonsa akan fuskarta yace, " ya daina?".
      "Ya daina, amma nahak'ura da abincinnan kawai, k'arasa mutafi".
      Jinjina mata kansa yayi, k'asan ransa kuwa yana jinjina k'ok'ari da jarumta irinta iyaye mata, amma ahaka har ake samun azzalumai irinsu hajia babba dake iya raba d'a da mahaifiya, wani bak'inciki ya tokare mak'oshinsa, daurewa yayi ya danne, Dan bayason hankalin Aysha yatashi.
    Amma dukda haka taga fuskarshi ta canja, badai tace dashi komaiba.
     Shima tashi yayi, Dan duk abincin yafitarmasa arai.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now