48

3.9K 305 1
                                    

  48

      Alhamdulillahi shirin biki ya kankama, anatama Inda zasu zauna fenti, can baya kusadasu ya Sultan, tunda aka saka ranar auren baffah yasakashi za6en yanda yakeso agina masa nasa wajen, yakuwa za6a.
     Tun sannan aketa ginin, hargashi ankammala cikin nasara.
     Kaf gidan kowa yanata shiryama wannan biki, dukda uban tafiya yace babu wani shagali daza ayi, acewarsa da kud'in daza 6arnatar wajen wani dinner, lunch, mother day.....etc, gamma ataimakama marasa k'arfi dashi.
    Baffa yaji dad'in hakan sosai, kuma yasaka masa albarka.
      Hajia babba kam ko a jikinta, da ayi dakar ayi duk uwar ubansu d'aya, yarantama basa wani nuna murnar Auren, saboda anhad'a yayansu da Aysha, amma sunata burin sai lokacin bikinsa da Aleeya, sukad'ai sukasan misuka shirya.

Nidai nace uhhhhmmm.😏

______________________
         Aysha kishirya gobe idan ALLAH yakaimu zaku wuce Kano keda gwagggonki.
     Lah mama da gaske?.
    Eh mana, can zaki koma, nasanarma baffanku ma, nima insha ALLAH ranar laraba zantaho gaba d'aya, kokinje Kano karkiyarda wani yabaki wani abin cushe-cushe ko wani ganyen magani kisha, banason shaye-shayen maganin matannan wlhy, Dan abubuwane masu illah, mutanene kawai suka Gaza gane haka, kingadai anan mamien ku tabaki tsaftatatttu itada Ammah, tunda nonon rak'umine Dana shanu sai kayan marmari  dasu aya Zuma kanimfari mazarkwaila dafanfar gyad'a dadai sauransu, wad'annan basa cutarwa tunda damacan ALLAH ya halatta mana shansu koda badan wannan manufarba, shiyyasama nahanaki shan nawajen bintu gaskiya.
     Nasan Yaya bazata bakiba itama, tunda bataso, kannena kawai nakeji da asma'u sai matar Ahmad, amma Na gargad'i Hafsat da fadeelah, tunda suma sunsan bamumusu wannan shashancin ba.
         Damu zauna 6ata lokaci wajan baku wannan shirmen da 6ata kud'inmu gamma mu nutsu wajen koya muku zaman auren da biyayya, maganin mata baya hana d'a namiji ya wulak'antaki idan yaso, idanda matanmu nada hankali dasun gane hakan, (wlhy naga matarda tahad'a kayan mata ta kwankwad'arma cikinta da yamma da daddare mijin yaji dad'insa, washe gari da safe sa6ani yashiga tsakaninsu ya sheshshek'ama fuskarta marika), shin Dan ALLAH maganin mata yayi riba kenan?, alokacinfa dasuke tareda sune kawai sukejin dad'in har miji yamiki wani sambatun banza, dazarar buk'atarsa tabiya shikenan anwuce wajen, wannan bazai hana yaci ubankiba, bazai hanashi cin zarafinkiba, bazai hanshi ya sakekiba, bazai hanashi yimiki kishiyaba, shin mata nawane suke amfani da kayan d'a'a amma basu fita daga cin kashin d'a namijiba, ga cututtuka dakiketa tanadama kanki wanda bazasu bayyana agarekiba sai lokacin da tsufa yazo miki, shin Dan ALLAH miye abin birgewa duk inda kika zauna kika tashi aganshi jik'e da ruwa, wannan wace iriyar masiface?, mutanan da maganin mata sukesha?, bama su sanshiba, amma suna zaune lafiya da mazajensu, wani aurenma sai anyi mace zata San mijinta, miji yasan matarsa, amma saikiga aurensu ana kiran shekararsa 80-70-60, kuma suna zaune lfy, ko sa6ani zakiga baya yawan shiga tsakaninsu.
          tsakaninku da ALLAH awannan zamanin aure nawane kekai shekara 10 kacal babu tashin hankali da masifu acikinsa, awannan zamanin inhar mace sukai zaman lfy Na kwana uku da mijinta acikin sati, to wlhy kwana hud'u cikin fad'ane, mafi yawancin abinda ke faruwa kenan, kuma koda yaushe kud'inki nagidan dillaliyar kayan mata, bakiciba, bakiba y'ay'anki sunciba, bakiba iyayenki sun sakamiki albarkaba, baki taimakawa marasashiba, saikije kisha abinda zai ruguza rayuwarki batareda kinsan hakanba, kedai kawai mijinki yaji dad'i, yaringa zunduma ihu lokacin dayake taredake, indan anhad'u gidan suna ko biki kiringa bama sauran mata labarin sambatun dayake miki da ihu, mata suna dariya ana cafkewa da miki jinjina kinci gari.
    Haba mata, wannan wace iriyar asarace haka, sirrin aurenkine agidan biki? Kaiconmu wlhy, ALLAH kuma ya tsinema duk ma'auratan dake fallasa sirrin aurensu, wlhy mugyara, keba karuwaba amma rayuwar aurenki tafi ta karuwai fita fili, wa'iyazubillah, Dan ALLAH mu kiyaye mata.
         Aysha karki yarda koda da kuskure hakan takasance dake, kada naji kada nagani.
      Kuka sosai Aysha keyi, tana jinjinama mama kai, kidaina kuka dan bama ayi komaiba, abinda yasa nabarki saboda kina kusadanine, akoda yaushe zan ringa nuna miki kuskuren abinda ke hana rayuwar aurenmu k'arko awannan zamanin.
    Tashikije ki kimtsa komanki, Dan duk za'a maidasu 6angarenku kafin natafi.
    To mama, ngd, tafita tana cigaba da kuka.
    Mama tabita da kallon tausayi, tana tausayama d'iyar tata da dududu bata wuce shekaru 18 ba,  gata da k'aramin jiki, bandama karatun kasashen waje ba irin namu baneba da saifama yanzu ayshar zata kammala Secondary nata, amma gata ayanzu hartana bautar k'asa (NYSC) d'inta

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now