12

4.2K 311 2
                                    

12

       Dr Abraham ne yay treatment nasu suduka, ancirema youseef bullet shida Oga  David, babu Wanda yasakebi takansu Oga David, ansakasu amak'argama, yaransa daban shima daban.
       Ya khaleel yakallisu Taheer dakowa yake zaune agalabaice, guys bara nad'anje gida, nanda 4hour's zan dawo, Adams zaikawo muku abinci bye.
     Kawunansu kawai suka iya d'aga masa, shima baijira cewarsuba yayo waje.

         Yau takasance weekend, duk ahalin gidan suna nan, bakajin komai sai hayaniyar su Arfat dake wasa a falo, sunbaje kayan wasansu sai tsalle-tsalle sukeyi.
     Aysha nagefe tana goge-gogen dining.
     Cikin fushi Hasnah tafito daga 6angarensu, wata uwar ashar data zundumama su Ashraff yasaka Aysha tsaida aikin nata tajuyo tana kallonsu, Hasnah tace Ku Dan ubanku bazakubar mutane suyi barciba? Kunbi kuncikamana gida da ihu tamkar goyon maguzawa! ko haka uwarku da uban naku suka koyar dakune? 'Yan iska gadon ta6ara........
      Tassss!!! Kakejin saukar mari akumatunta, agigice tadafe kuncinta, Dan marin yazo mata abazata, Aysha kanta daba ita aka maraba saida rintse idanunta.
    Kafin Hasnah tagama ganin mai Marin nata yacigaba da dukanta, ball yake da ita kamar afilin kwallo, tuni kururuwarta tacika gidan, sai kwala kiran sunan momy take cikin kuka da neman ceto.
    Babu shiri ahalin gidan sukayo waje, kowa yafito yay arba damai dukan hasnah saiyaja tunga gefe yana zaro ido, Ammah da Baffah ne k'arshen fitowa, sai momy abayansu, cikin tsabagen masifarta tace ubanwaye yake dukarmin yarinya? ta ture Hameedah dake kan hanya takutso kai tsakkiyar falon.. itama kanta idanu tazaro waje da mamakin yaushema yawo gidan?, ganin duk garatan samarin gidan babu mai yunk'urin kwatar mata yarinya ahannunsa yasata kiran sunansa cikin tsawa!.
     Ibraheem!!!!!.
Cak yatsaya daga dukan nata, kansa na kallon k'asa, sai huci yakeyi dan 6acin rai. kowa yayi cirko-cirko, kaf k'annen nasa babu mai jarumtar matsawa kusa dashi. Baffah yatako ahankali har inda yake tsaye, jawosa yayi jikinsa ya rungume, ahankali yasauke wata nannauyar ajiyar zuciya, sun sami kusan minti 3 ahaka sannan yad'agoshi, fuskarnan tayi jajur, abinka da mutum mai haske, girgiza kai baffah yayi, sannan yace, "Mu'azzam! Miya farune? Yaushema kadawo gidan? Yay maganar yana kamo hannun sa da'aka nad'e da bandeji.
          Haryanzu ransa a6ace yake, Dan haka ya girgizama baffah kai kawai saboda bazai iya maganaba. ganin haka yasa Ammah k'arasowa inda suke, hannunsa takama tana fad'in zoka zauna kahuta kaji Iro!. cije le6ensa nak'asa yayi, idonsa nakan momy dake rungume da Hasnah tana 6arzar kuka haryanzun. harya farabin Ammah saikuma yatsaya, cikin k'ara hasala yadakama Hasnah tsawa!, k!! Wlhy idan bakima mutane shiruba saina ida 6allaki 'yar iska kawai mara mutunci!!.
     Da sauri Hasnah tasaka hannunta ta toshe bakinta tana k'ara k'ank'ame momy.
     Momy takallesa itama cikin 6acinrai, dukda takasa cemasa komai amma idanunta sun nuna alamun gargad'i da tsana agaresa, tayi kwafa tareda kuma rungumo Hasnah jikinta.
      Shima iska yahuro daga bakinsa, yacigaba dabin bayan Ammah dake rike dashi har yanzun.
      Haka kawai Aunty Amatullah taji zafin kallon da momy taima Khaleel, cikin sanyin jiki tanufi hanyar kichin.
    Duk bidirinnan da akeyi Ummee amarya batako lek'oba, tana d'akinta, kuma tanajin duk hidimar da akeyi.
     Aunty Mamie kam tana wanka, tak'agara tagama tafito dantaga mike faruwane?.
  
Ruwa mai sanyi Aunty Amatullah tamik'ama Khaleel boda zufar dayaketayi, hannu  yasa yakar6a tareda sakar mata sassanyan murmushi, muryarsa a raunane yace, "ngd lil Ama..
     Itama murmushin tamasa.
      Wannan lamari bak'aramin kule zuciyar momy yayiba, wato saboda tsabagen munafinci ga yarinyarta yadoka dukya fasa mata jiki da sassafen nan, amma babu Wanda yace da ita koda sannu, saishi dayayi ta'asar suke bama kulawa.
       Ture kan Hasnah tayi daga jikinta, azafafe tamik'e tak'arasa inda suke, harya kai kofin ruwan bakinsa ta ka6eshi yafad'i ajikinsa, gabad'aya ruwan yazube MASA, dasauri yarintse idonsa saboda sanyin ruwan dake ratsa masa jiki.
       Tanuna aunty Amatullah da d'anyatsa tana fad'in k! Dan uwarki  Bilkeesu ahir d'inki dashigarmin rayuwar 'ya'ya, tsafin na Uwarki haryakai kishayarmin dad'ana agabana? Wlhy ko Bilkeesu bata isaba, ALLAH yafiku, dama nasan uwarkuce ke saka Ibraheem yana tsanar 'yan uwansa ciki d'aya, annamimai, insha ALLAHU aniyarku saidai tabiku kuda Uwarku marasa tarbiyya......
      Da Sauri Baffah yakatseta.... K! Laurah! Wai miye matsalarkine?, yamzunan saboda ALLAH bazakiyi bincike akan hukuncin da mu'azzam yayiba? Dan Nasan yanada dalilinsa, haka kawai bazai kama dukan hassana ba aii. Kuma naga aii yanda hassanah take d'iyarki hakama Mu'azzam d'ankine bare kidasama mutane kambun masifa, kokunyar yarannan bak'yaji? Kiringa cin mutunci mahaifiyarsu agabansu? Yanzu miye laifin Bilkeesu danta nuna kulawarta ga Mu'azzam?.....
    Eh aibazaka ganiba tunda kaima sunanka yana wajen bokan saman tsauni, wlhy kuma afitamin hanyar yaro, kokuma ran uban kowa ya6aci agidan, munafincin banza dawofi.
    Kaikuma sallamamme kasameni inajiranka.....fuuuu takama hannun Hasnah dake d'ingishi suka shige 6angarenta, Husnah da Hameedah Na take musu baya.
       Babu Wanda yakuma cewa komai.
     Ammah ta dafa kafad'ar khaleel dayay k'asa da kansa, tace tashikaje kacanja kayanka kaji iro, kacigaba dama mahaifiyarka Addu'a ALLAH ya shiryeta.
       Baice komaiba yatashi yanufi 6angaren samarin gidan. Suma baya suka take masa, ya Sultan ne kawai babu, yaje bauchi.
     Suma 'yan matan kowa zame jikinsa yayi suka koma d'akinsu, ammah ma 6angarenta tatafi, ganin haka su Aysha suma suka sulale sudasu gwaggo bintu sukai kichin.
    
      Amal tace wlhy ya khaleel yana bani tausayi, aikin nan nasu yanada had'ari sosai, bansan miyasa yaza6eshiba?.
    Wlhy bake kad'aiba cewar Hamdiyya, ya khaleel yanada kirki, kwata-kwata  ba halinsa d'aya da momyba, duk d'akinsu yafi kowa mutunci, shidai barshi darashin son raini, bayason arainashi.
     Shuhuda tace, "kumsan ALLAH ya khaleel yafisu ya Muhseen kirki, gashida son 'yan uwansa, indai ka iya zama dashi zakaci riba, dukda kasancewarsa murd'ad'd'en mutum mai tsatstsauran ra'ayi.
     Naseeba tace gaskiya kuka fad'a wlhy, shi ya khaleel kaifi d'ayane, kuma yanason had'inkan gidannan dukda mahaifiyarsa batason haka, bazan 6oye mukuba nadad'e inason ya khaleel amma tsoron Momy yasa nasama zuciyata salama.
    Tab wlhy kin taimaki kanki, aii ya khaleel inba matar dazataci uwarsu Aunty Hameeda dasu aunty zuwairah ya auroba tofa akwai matsala, bazata ta6ajin dad'in zama da momyba agidannan.
    Wlhy hakane Amal.
   Hakadai sukaita hirarsu.

   Tasleem kam tuni tatafi kaima Aunty zancen abinda yafaru.
   Fitowarta kenan daga wanka Tasleem tashigo d'akin, fad'awa tayi jikin aunty tafashe da kuka.
     K! Miye hakane wai? bana hanaki halinnanbane wai Tasleem? minene yafaru kika shigomin da kuka?.
     Aunty ya khaleel ne yaji k'aton ciwo a hannunsa, kuma yadaki aunty Hasnah, Momy sai fad'a takeyi Dan Aunty Ama... tabashi ruwa yasha.
    Da sauri Aunty tace, "ciwofa Tasleem? yana ina yanzu?.
    Yana 6angarensu cewar Tasleem tanacigaba da sharar kwallah.

    A gurguje Aunty tazura doguwar riga tafito, afalo tawuce su Hamdiyya dasuka fito yanzu, Naseeba tayi dariya, tosu auta sunkaima aunty gulma, dama nalek'ata tana wanka.
    Shuhuda tace ALLAH Sarki aunty, yanzu dukzata rud'a kanta, dukda wulak'ancin da Momy take mata agidannan baya hanata kulawa ga ya khaleel.
     Amal tataso daga kujerarta tadawo tsakkiyarsu Shukurah, sotake tayi gulma, amma bataso su maleeka da Tasleem suji, cikin k'asa-k'asa da murya tace kunsan wani Abu?, kai suka girgiza mata, tacigaba da fad'in wlhy ina mamakin yanda aunty take matuk'ar damuwa da al'amuran ya khaleel, nifa sainaga kamar tafi Momy sonsa.
      Wlhy gaskiyarki Amal, nifa nadad'e inaso namuku gulmarnan amma inajin tsoro,  sainake gani kawai had'uwar jinice, kugafa yanda Momy take nunwa batason aunty acikin agidannan k'uru-k'uru, amma yanda aunty take nuna kulawarta akan ya khaleel kosu ya Sultan batama haka.
    Shuru sukayi suna nazarin maganar amal, shuhuda tace kumafa gaskiyarku amal.
     Naseeba zatayi magana Ammah tashigo falon, cikin rakad'inta tace to magulmata halan annamimancina kukeyi?.
    Gaba d'aya sukayi dariya, Hamdiyya tace mumun Isa gulma da uwar masu gida.
     Amma tad'ingiso 'Yar k'afarta tana fad'in yonasani.
       Nanma dariya sukayimata.
      Shuhuda tace yauwa Ammah Dan ALLAH munada tambaya?.
    ALLAH yasa nasani to.
   Kinma Sani insha ALLAH.
   Ammah kid'an bamu tarihin agidannan mana kafin haihuwarmu.
    Dariya Ammah tayi, kai kujimin magulmatan yara, mikuma yakawo wannan zancen?.
    Bakomai wlhy Ammah, munasonjine kawai.
   Shikenan zan Baku, amma kubari sai ALLAH yakaimu dare.
    Murna sukaitayi harda tsallensu, Ammah namusu dariya.......🖊

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now