28

3.1K 311 0
                                    

2⃣8⃣

A k'ofar jirgin yatsaya domin yazone wajen wani abokinsa Captain ne, shinema zai tuk'asu Aisha zuwa Canada.
     Gaban meerah ne yafad'i alokacin data hangi john, mayafinta takuma ja tarufe fuskarta sosai, dama Aysha barcima takeyi.
     Abokinsa yak'araso suka gaisa cikin rungume juna.
    John yatambayesa ko akwai jirgin dazaije Africa a yau?.
    Kai a'a gaskiya, inagama gaba d'aya week d'inan babu wani jirgi dazaije Africa, amma next week akwai mai zuwa Africa, zai sauka Nigeria babban birnin k'asar Abuja.
     Murmushi yayi yace OK, inason sanin list d'in masu tafiya aranar, zanshigo kafin jirgin yatashi.
   OK babu damuwa.
 
Ya Naufal na'a wajen 6uyansa yahango fitowar John, ajiyar zuciya mai k'arfi yasauke, tareda fad'in *_Alhamdullahi alah kulli'halin!_*.
     Saida ya tabbatar john yabar airport d'in sannan shima yatafi.
    Kaitsaye gidansu Anty glory yanufa.
    A k'ofar gidan ya iske motar john. bayan yayi Knocking d'in k'ofar besi tabud'e masa, cikin mamaki take kallon Naufal d'in, shikuma yafuske abinsa yana tambayar ko meerah na nan?.
        Besi tace aimuma nemansu akeyi, harma ana shirin zuwa gidanka ko sunacan.
    A tsorace ya Naufal yace banganeba? Inasu meerah sukedashi bayan nan?.
        Anty glory datakejin zancensu sama-sama talek'o dantaga wanene?, ganin Naufal ne tace Kaine? Dama su meerah basa tare dakai?.
     Wai wane zance kukemin hakane? nifa kuna wani juyamin tunani, Ku warwaremin abinda ke faruwa mana.
      OK kashigo to, Anty glory tafad'a dan hango gaskiya k'arara atareda Naufal.
       Sunmasa bayanin duk abinda yafaru, yayinda Naufal yanuna matuk'ar shiga tashin hankali, yace shin yanzu duk inda suke zuwa anje basa nan?.
     Duk anje, mu munma fara zargin kodai sun gudune? yanzu haka daga airport nake, amma an tabbatarmin babu wani jirgin daya tashi zuwa Africa a yau.
       John ne dake zaune yanata kora giya yayma ya Naufal wannan bayanin, daka gansa kasan yana cikin damuwane.
       Dan john bak'aramin so yakema Aysha ba, baima San yana sonta da gaskiyaba sai ajiya data ku6ce masa, babban tashin hanaklinsa karsu tona masa asiri, tabbas kashinsa yagama bushewa kawai.
      Ya d'aga kwalbar giya gaba d'aya saida ya shanyeta tas sannan ya ajiye.
    Ya Naufal ma duk yanuna matuk'ar tashin hankalinsa, su Anty kubra sai lallashinsu sukeyi daban hak'uri, suna karfafa musu guywar za'a gansu, dansu meerah basuda Samar Baron k'asar su kad'ai.
    A can k'asan zuciyar ya Naufal kam dariya kawai take cinsa, dannewa kawai yakeyi.

*_Canada_*
           Jirgimsu Aysha yasauka a Canada, Dady Momy da k'annen ya Naufal uku sukazo tarbar su meerah.
       Basuwani sha wahalar ganeauba, saboda matuk'ar kama da ya Naufal keyi da dadynsa, suma su Dady ya Naufal yatura musu hotunansu Aysha, danhaka suka ganesu dawuri.
     Tarba ta mutunci suka samu awajen iyayensu Naufal, mahaifiyarsa baturiya k'yak'yk'yawa, hakama k'annensa duk kama suke da ita, shikad'aine yake kama da babansa.
      Komai cikin tsari yake agidansu Naufal, sosai tsarin familie nasa yabirsu Aysha, al'amuransu akwai fahimtar juna kam, ga komai cikin ilimi, saidai sunkula akwai k'arancin kula da addini ga mutanen gidan, dukda mahaifiyarsu Ya Naufal ma ta musulunta.
           Ifteehal k'anwar ya Naufal ta uku, itace sa'ar Aysha, shekarunsu d'aya, saidai banbancin launin fata da yanayin rayuwa, Dan ifteehal tanada girman jiki babu laifi 'Yar lutiyace, amma bawai sosaiba.
       
Baradai namuku gwari gwari, gidansu ya Naufal su 7 ne, dadynsu momynsu sai ya Naufal shine babba, sai Maheer, Ifteehal, Safwan, Iklaas.
   Akwai k'aunar juna kam tareda jama'ar gidan, komai nasu abin birgewa daban sha'awa.
         Mahaifiyasu ya Naufal (Momy) akwai kirki, tajawo su Aysha jikinta sosai yanda zasuyi sabo dasu.

Bak'aramin tashin hankali su Anty glory suka shigaba alokacin dasuka gama bincike d'akin su Aysha kaf, sunkwashe dukkan wani Abu Nasu mai muhimmanci, wannan yana nuna alamar tabbas sungudu.
    Wata takarda Anty kubra taci karo da ita k'ark'ashin filo, da hanzari ta d'auka ta warwareta.
   Kowa yay shiru ana sauraren abinda ke ciki.

_Kar ku nememu. domin bazaku ta6a Ku samemuba, munbarku har Abadan, mun muku nisa, abinda kuma kuka aikata akanmu, munbarma ALLAH ikonsa, yafimu sanin yanda zaiyi daku._
   _Ku sanarma Naufal ma ALLAH yaymasa sakamako da abinda yamana, Dan ubangijinmu yafimu sanin abinda ya cancanta ga mutane irinsa._

Wannan shine kad'ai abinda ke'a rubuce.
        Jikin kubra da glory sai rawa yakeyi, john kam aii ya daskare a zaune, ayanzu kam yadaina zargin Naufal d'in, danshi da gabad'aya zarginsa yanaga Naufal, harma yasaka wasu mutane sufara bibiyar Naufal.
   Ashe bashine yataimaki su meerah ba, to wanene ya taimaka musu? tabbas da taimakon wani suka gudu, kuma yanada tabbacin basubar k'asar nanba, suna aciki tabbas, lallai yad'auki alk'awarin nemosu, yana samunsu kuma kashesu zaiyi kawai.
       Mutanen dayasa suringa bibiyar Naufal yakira, yace subarsa yajanye aikinsa akan Naufal d'in.
     Glory kam da hanzari tanufi d'akinta tafara binciken box d'in datake Tara dukkan bisar yaran da'aka kawo, jikinta rawa yafarayi alokacin datayi tozali babu ta Aysha da meerah, jitayi jiri kawai naneman kwasarta k'asa, tayi saurin dafe gado tazauna k'asa ragwaf.
    A wannan halin kubra tazo tasameta, dasauri ta'iso gareta tana tambayar ba'asi.
        glory bata iya bata amsaba, sai tura mata box d'in tayi gabanta.
      Itama bak'aramar razana tayiba, lallai kam lik'insu Na gab da 6ulewa, dolene ad'auki matakin gaggawa kafin komai ya lalace.
    Waya ta d'auka tashiga kiran duk wani mai fad'a aji a k'ungiyarsu, ta tabbatarma kowa da guduwar su Aysha daga hannunsu.
     Dayawansu hankulansu yatashi, kuma sun fara haramar d'aukar mataki.

Nace to ALLAH Na nan aii.😰

______________________________
             Dan ALLAH Alhaji kafahimceni mana, ai wannan abin kunyane, kana haihuwa 'ya'ya Na haihuwa.
          Nifa ALLAH inajin kunya.
       Murmushi baffah yayi, idonsa kam akan mama, yace fad'ima kenan, nikam azatona murna zakiyi da cikinnan, amma sainaga sa6anin haka daga gareki.
    Nikuwa kinga yanzu babu wani abinda yake sakani farinciki kamar natuna kinada ciki, zaki haifamin yara, koba komai zanga k'ananun yara nima agidana, nad'auka nayi farinciki.
     Humm duk yarannan har 22 da ALLAH yabaka baka godeba kenan, kuma duka shekararsu Nurridden nawama? Basufi 5-6 bafa, aibasukai girman daza'ace anfara kwad'ayin k'ananun yaraba.
         Haka kike gani dai, Dan ALLAH mubar zancennan, kinsandai da hankalina da girmana bazan amince kizubarmin da cikiba, inason kayana, dukda inada yara 22 bawai nagaji da haihuwar baneba, matannan duk tsaida haihuwarsu sukayi saboda rad'in Kansu, bada kuma yawunaba, Bilkeesu Ce kawai naga yakamata tahuta saboda wahalar datasha a haihuwar Tasleem da Ummunoor, nace a tsaida haihuwar alokacinda ta haifi Ummunoor, daga bayama kuka taitamin akan tanaso itadai tacigaba da haihuwarta, da k'yar nasamu tahak'ura, shima saida likitan yamata bayanin illar da rashin hutawar zai haifar mata sannan.
     Amma kinga laura dakanta tatsaida haihuwarta tun aihuwar 2wins, hakama Saudah.
       To  kekuma ALLAH yabanike maimakon kicigaba da haifamin saikice a'a, ina son cikina, kuma banason kik'ara min wata magana akansa wadda zata iya kawomana 6acin rai.
          Shikenan bazan sakeba, amma gaskiya nikam inajin kunyar rainon ciki acikin manyan 'ya'yanmu.
          Abin yaso bama baffa dariya amma saiya dake, 'yace OK babu damuwa, saiki shirya mutafi Turkey kawai bayan bikinsu Sultan, idan kika haihu saimu dawo.
          Shiru mama tayi tana nazarin maganar, ganin haka baffah yace nabaki dama kije kiyi tunani akan hakan...................✍🏿

CIKI DA GASKIYA......!!Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu