70

4.9K 334 1
                                    

70

              Ya khaleel baisan hidimar da akeyiba, shi gaba d'aya hankalinsa nakan Aysha, ya kar6i ruwan da Anty Amatullah ke basa ya wankema Aysha baki, duk jikinta ya saki, sai langa6e masa ajiki takeyi, (kunsan dai yanda amai ke saurin galabaitar da mutum), bare Aysha datakeyi tunda daddare.
      Anty Mamie ce tayi azamar k'arasawa garesu, ''hajia Atine lfy dai ko? Naga d'iyata Na kuka?".
             "Hajia Bilkisu mudai shiga daga ciki wajen Alhaji Abdallah, lfy naganku waje tsaitsaye?".
         " wlhy Aysha ce matar babana khaleel babu lfy, shine zamuje asibiti, amma kumuje ciki, alhajin yana nan aii".
        Wajen Ammah datun d'azun itama idonta nakan mufeedar Anty Mamie ta k'arasa, saida ta rissina sannan tasanar mata sunzo wajen baffane.
        Ammah ta ta6e baki, ''to Bilkeesu, kiyi musu iso, nasandai lalatacciyar nan ta tafka halin uwartane gidan mutane".
     Anty Mamie dai batace komaiba, tamusu jagoranci zuwa 6angaren baffah. Saida tafara Shiga ta sanar masa sannan tabasu izini suma.
          Dukda daga baya ya khaleel yaga mufeedah amma bai maida hankalinsa kantaba, yashige mota da matarsa Na jikinsa, Hafez nagaba zai tuk'asu. Harya tada motar mama tak'araso wajen.
        "Babanmu inaga kabar su Amatullah saisuje da Ayshan asibiti, kaga ga mufeedah dabak'i, ba'asan mike faruwaba, nasan kuma dolene anemeka amatsayinka Na babba".
         Marairaicema mama fuska yayi, please mama kibarmu mutafi, wlhy Aysha ta galabaita, aii su Sultan suna nan, kuma uncle ma'aruff ma yana nan, mama Dan ALLAH jikinta k'ara zafi yakeyi".
       Tamkar mama tayi dariya, amma saita danne, tace, " shikenan, kuje, amma idan kaga da sauk'i kudawo gida".
      "To mama".
Hafiz yaja mota suka fice, Amatullah na agaba, shikuma yana baya rungume da Aysha.
      Anty shukurah ma batabi takan abinda yadawo da mufeedah ba tashiga mota itada Ramadan sukabi bayansu.
      
Duk rugund'imin da akeyi agidan akan ciwon Aysha hajia babba naji amma kota kula, sunatama shan hirarsu da sauran bak'inta, hakama Anty zuwairah tanaji amma tayi kunnen uwar shegu, saima k'ok'arin had'a sauran kayan mufeedah takeyi wai su najwa suje su kaimata. Fitowar su Najwa zasuje gidan mufeedah ne sukaji k'ananun magana Na tashi akan dawowar mufeedar, dasauri suka koma suka gayarama hajia babba.
          Da Sauri tamik'e tana fad'in, " ke shashasha mikike fad'ane?".
      Baki najwa ta zun6uro gaba, "Niba shashasha baceba, kajimin momynnan, bajinayi ana gulmaba awaje, wai tana 6angaren baffah Anty mufeeyn".
     Da sauri Momy da zuwairah suka nufi 6angaren baffa, kotakan jama'ar tsakar gidan basubiba.
        Mufeedah Na k'asa, 'yan rakiyarta da baffa da ammah Na zaune.
     Wayace a hannun baffa yana kiran Ameenudden, Dan yafison ayi komai a gabanshi.
      Babu dad'ewa ameenudden yad'aga, cikin ladabi ya gaida baffa. Baffah ma ya amsa cikin kulawa, yace, " yarona Ameenu kana inane?".
        "Baffah ina gida".
      ''gidanka konan gidanku?".
       " a'a gidana".
  "Idan ban takurakaba kazo INA nemanka".
          " to baffah inazuwa".
     Dama ashirye Ameenu yake, yasan dolenen anemeshi, tunda mahaifiyarsa da yayyensa biyu kawai sukasan miya faru, wad'anda suka raka Mufeedah kuwa Yayar babansace da k'anwar mamansa.
    Babu dad'ewa saiga aminudden.
         Cikin girmamawa ya gaida kowa dake falon, Yakoma kusada mufeeda k'ad'an ya zauna.
   Baffah ya kalli Anty Mamie, "Bilkeesu ina Mu'azzam da Sultan?".
        " babana yatafi kai Aysha asibiti, saboda tanata amai, saidai akira Sultan d'in".
      ''Ya salam, shine ba'a sanar daniba, yaushe abin yafaru".
       "Kayi hak'uri baffansu, wlhy dukmun rud'ene".
       ''To ALLAH yabata lfy, bara agama da wannan matsalar saimu bisu, kiramin sultan da Mujahedeen awaya........
       Shigowar hajia babbane yasaka kowa waigawa ya kalleta, mufeeda tatafi da gudu tafad'a jikinta tana kuka.
     Tsawa baffa yadakama mufeedah, ''Dan ubanki dawo ki zauna, kafin Na sassa6a miki kamanni".
          " tofa zaka raba 'ya da uwane?".
     Banza baffah yayma Momy, kuma babu Wanda yasake tankawa, dukda surutai da Momy ke saki marasa dad'i, wai ba'a kirataba, amma ancika mak'iyanta da falo sun saka mata 'ya tsakkiya.
       Cik'in 'yan rakkiyar mufeeda hajia Altine tace a lallai, Ashe da dalili shiyyasa matarka babu tarbiyya Aminu?".
        Kowa dai yay shiru ba'ace komaiba, harsu ya Sultan suka shigo.
    Ananne baffah yay gyaran murya, tareda sallama, yace, "aminuddin mike faruwane?".
     Kafin yayi magana hajia babba ta kar6e, wlhy bazai yuwuba, saidai kowa yafice yafad'a dagani saikai da mufeeda, amma baza'a fad'i komai gaban kishiyoyinaba".
      Tsaki baffa yayi, yad'auki waya yakira mama da umme amarya, yace suzo yana nemansu.
       Cikin k'uluwa hajia babba tafara zuba jaraba.
     Amman Ce ta taka mata birki, Laure wlhy inbakiyi shiruba yanzu zakibar falonnan, kokuma nasaki nadama.
     Saida Momy ta gatsina baki sannan tayi shiru, tasandai wacece ammah, bata d'aukar raini.

CIKI DA GASKIYA......!!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora