7

4.4K 325 0
                                    

0⃣7⃣

      Harsuka shige Aysha dasu bishirah nabinsa da kallonsun sha'awa, bak'aramar damuwa hakan yasaka Aysha ba, harda d'an kukanta sakamakon tuna nata ahalin itama, harga ALLAH tana kewar gida da 'yan uwanta, dama bikinsu Yaya Fhadeela take kwad'ayin zuwa kuma and'aga sainanda watanni uku.
    Basu sake jin d'uriyar mutanen gidanba har dare, sai bayan isha'i ne aka aiko Nureedeen yakira Aysha da bishirah.
     
   Da sallama suka shiga katafaren falon, dukda sunsan bama lallaine wani yajisuba, 'yan matan gidanne kawai ke kallon film. Su Aysha sukamusu sannu.
    Duk suka amsa musu cikin k'yak'yk'yawar alak'a, dansu ba'a musu tarbiyyar wulak'anta 'yan aikiba.
   Bishirah tace Anty Amal gamu.
      Kai bishirah wayace ina kiranku?.
    A'a dama Nuriddeen ne yace muzo, tonazata kokune ke kiran. Bamu baneba inagato Aunty ce ko Ummee, amma kuzauna ina zuwa.
   Amal namik'ewa saiga Aunty Mamie tafito daga 6angarenta, Amal tace yauwa Aunty kece kika aika Nurri kiransu Aysha?.
   Eh nice, suna inane?.
    Aysha da bishirah sukataso suna fad'in gamu Aunty Mamie.
    Yauwa kuzo muje nad'an sakaku wani aiki nan.
       Aunty Mamie nagaba su Aysha nabinta abaya harzuwa 6angaren samarin gidan, Wanda yau shine farkon zuwan Aysha, Ya Zunnurain da ya Mujahedeen da Hafeez ne kawai afalon suna kallon kwallo, sai Musleem dakecan gefe yana duba books, da alama wani bincike yakeyi ko aiki.
      Duk suka gaida Aunty Mamie, sannan ya mujahedeen yace Aunty Mamie baki aikomin maganinbafa.
    O namanta wlhy Mujaheed, amma miyasa baka tunaminba? Haryanzu wajan namaka ciwone?.
    Eh wlhy yanayi, d'azufa har zazza6i yakusa yasakarmin.
   To ALLAH ya sawak'e, Hafeez jeka d'akina saman madubi kad'akko box d'inan kakawo masa yaduba.
    To aunty, Hafeez yafad'a yana mik'ewa.
   Su Aysha sukaima ya mujahedeen sannu, kansa kawai ya jinjina musu, danshima akwai d'ankaren miskilanci.
         Aunty tace babanafa?.
     Yana d'akinsa, cewar ya Zunnurain.
      A'a ahakan kuma yazauna? Bayan yace, ''d'akin duk datti.
      'Yar dariya mujahedeen yayi, to aunty aikinsan halin kayanki dai, amma baima dad'e dashigaba tunda yanzun muka dawo masallaci.
   Ok, bara baduba, inasu Muhseen?.
       Sunje wani waje shida ya Ramadan.
Sultan fa?.
baffah ya aikesa inaga.
       Ok.
   Anty tanufi d'akin khaleel, harta fara tafiya tagasu Aysha BASA binta, tace kutaho mana.
    
Saida tamasa Knocking sannan yabud'e k'ofar, sanye yake cikin wando da Riga ash colour, rigan mai bud'ad'd'en k'irjice, amma yasaka vest ak'asa, wandonma iyakarsa guywarsa, sai silifas bak'i ak'afarsa, wani ni'imtaccen turare yabigi hancin su Aysha, suduka saida suka lumshe idanunsu.
    Yana ganin aunty Mamie yasaki murmushi, cikin girmamawa yace Aunty Mamie kece?.
    Eh babana, d'akin za'a k'ara gyara maka nasan kana iya cewa kakasa barcima aciki.
    Wlhy kamar kinsani aunty, yanzun Yakama shirin tafiya d'akin sultan nakeyi Dan nikam k'yank'yamin d'akinnan nakeyi,  kokad'an ba'amasa wani gyaraba.
      A'a babana, aiko nagasu Hasnah sungyara d'azun da safe.
    'Dan tsaki yaja, yace Aunty miwad'an Nan yaran suka iya banda rashin mutunci yay maganar tareda komawa cikin d'akin, Aysha da bishirah sukabi bayansa shida aunty.
   Mamakine yakashe Aysha, Dan itakam bataga wani dattiba awannan d'akin, gashinan Fe's, saidai 'Yar k'ura, wadda hakan yana nufin Wanda yay gyaran d'akin yanada gandar tsayawa k'alk'ale Abu, amma babu wani dattifa.
           Aunty tace to babana gasunan zasu sake gyara maka, saika nuna musu ko.
    To Aunty sufara da toilet.

Tsaf Aysha tagyara toilet d'in sai shek'i yakeyi, daidai da bokiti da butoci saida tawanke masa k'al, har tayils d'in jikin bangon bayin kanshi yad'auki haske, turarirrika tagani kala-kala masu saka bayi k'amshi, suma tad'auka duk tasaka.
      Koda tafito d'akin babu bishirah, abin yabata mamaki, shikad'aine zaune akujerar d'akin yana danna wayarsa, dukji tayi tatakura, hakadai tafara cire zanin gadon, kunfar data had'a abokiti tatsoma k'aramin tawul aciki tafara goge fuskar gadon dashi, saida ta goge tsaf yanata k'yalli sannan tad'akko zanin gadon zata mayar.
    Daddad'ar muryarsace tadaki kunnenta, yace, "karki mayarmin deity bedsheet d'in nan a bed.
    d'agowa tayi tana kallonsa, saidai amamakinta haryanzun kansa ak'asa yake, yana danna wayarsa. wajen mintina uku baisake cewa komaiba, itakuma Aysha tana kallonsa kamar tasami TV.
     K! Karfa ki cinyeni, kinwani k'uramin kwala-kwalan idanuwan kinnan.
         Aysha tayi k'asa da kanta cikeda kunyar kamatan dayay tana kallonsa.
       Cikin k'asaitarsa yamik'e zuwa Waldrop d'insa, yad'ako bedsheet Fari tas, saman gadon ya ajiye yakoma inda yataso yakuma zama.
      Aysha tad'auka ta shinfid'a, bata sake kallon inda yakeba harta kammala komai, yarage mata shara da mopping, tanaso tamasa magana tanajin tsoro, kusan mintuna 5 suna ahaka, saiga bishirah tashigo da tire, inda yake taje ta ajiye masa, cikin girmamawa tace ya khaleel gashi.
   Shiru bai amsaba har wad'ansu seconds kuma haryau waya yake dannawa, sannan zuwa can yace waye yadafamin?.
    Murya narawa tace Aunty Amal ce.
    Kansa kawai ya jinjina mata, yay mata nuni da hannu alamar tatafi.
    Aysha kamar tayi kuka, tanason yima bishirah magana amma tanajin tsoro.
       Waike tsayuwan yana miki dad'ine?....
    Muryarsa tadaki kunnen Aysha.
     Cikin in ina tace um....um ....dama shara ne yarage da mopping zanyi, shine saikuma naga.....um....
        'Dago dara-daran idanunsa yayi yasauke akanta, bak'aramar figigita Aysha tayiba, dan yamata kwarjini sosai, ga fuskarnan a d'inke babu alamar sauk'i.
    Yaja gajeren tsak'i  tareda janye idanunsa daga gareta, yace kinga idan zakiyi kiyi, inkuma bara kiyiba kiyita zama awajen useless kawai.
        Cikin taushi muryar tasa ke fita, amma shi adole fad'a yakeyi.
     Ran Aysha yasosu, harga ALLAH batason dizgi, amma takula wannan mutumin bashida kirki, yandama taji yaran gidan suna hirarsa yawuce nan.
         Shararta tafarayi, saida tazo inda yake sannan yakwashe k'afafunsa yamaida saman kujerar.
   Daganan babu Wanda yasake kula d'an uwansa, harta kammala komai.
   Yanzuma saida tabaje ko ina da k'amshi sannan tacemasa tagama, baice mata k'alaba, itakuma tagaji da tsayuwa takama hanya zata tafi, harta kama handle d'in k'ofar yace, "k! Zonan.. 
        Gaban Aysha Na dukan uku-uku tadawo inda yake, durk'usawa tayi agabansa cikin sanyinta tace gani.
     Tashi ki had'amin shayinnan.
    Mik'ewa tayi daga durk'uson taje inda k'aramin table d'in glass d'in yake tafara had'a masa shayi.
    Knocking d'in k'ofar akayi, dak'yar ya iya bud'e baki yace kowaye yashigo.
     Hameeda Ce tashigo ko sallama babu.
     Ya Khaleel kazo inji momy.
    Wata uwar harara ya maka mata da wad'annan fararen idanun nasa, tayi k'asa dakai tanad'an zun6uro baki.
    K! 'Yar iska baki iya sallamaba ne ko!. fitarmin ad'aki kona 6allaki stupid girl kawai.
      Saida ta ballama Aysha harara sannan tafita tana k'unk'uni k'asa-k'asa, dantasan inhar yaji kashinta yagama bushewa.
     Shikam tana fita yaja wani wawan tsak'i Wanda yatsorata Aysha, ALLAH yasotama tagama had'a shayin, yanzukam koneman izininsa batayiba tafice da saurinta.
     Shima baice da ita komaiba yad'auki shayinsa yahausha, ko zafima bayaji.
    Saida yagama tsaf sannan yacanja kayansa zuwa jallabiya fara tas yatashi yafice.
    Wajen baffansu yafara zuwa, saidai bayanan yafita, saikuma yashiga 6angaren Ummee Amarya.
    Tana zaune afalonta hakimce, sai Nureedeen da Ummunoor da Asharaff dake wasa agefe, da 'Yar fara'arta tace a'a khaleel ne ak'asar tamu?.
      Shima guntun murmushi yayi yana fad'in eh wlhy Umme, munsameku lafiya?.
     Lfy lau muke, ya aikinku?.
    Alhmdllh Ummee.
Daganan sukai shiru, Dan babu wani sabo tsakaninsu da ita, Su UmmuNoor dasuka hangoshi yanzun suka taso da gudu sukayo kansa.
    Yanason k'annen nasa, yataresu da murna, duk gaidashi sukayi, Asharaff yace Uncle! Muma yaushene dadynmu zasuzo shida Maah-Maah d'inmu?.
     d'an murmushi yamasa tareda Jan kumatumsa yace my son zasuzo suma soon insha ALLAH
        tuni Asharaff yamik'e yana tsallen murna, shidai Khaleel sai murmushi yakeyi.
     Yamik'e yanama Umme saida safe, cikin kulawa ta amsa masa.
     Daga nan sai 6angaren Ammah tsohuwa............🖊

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now