6

4.7K 355 1
                                    


6⃣

      Gaban Aysha sai fad'uwa yakeyi sakamakon kiran da hajia babba ta aiko karime Tamata. harsuka shiga falon tana addu'ar daduk ta iso bakinta.
     Hajiya babba nazaune tareda wata hamshak'iyar mace, daganinta kasan naira ta zauna.
   Karime tarissina tana fad'in hajia ga Ayshar nan.
    Kai kawai hajia babba ta gyad'ama karime alamar taji.
      Karime nafita daga falo Aysha ta durk'ushe tana gaishesu, babu Wanda ya amsa acikinsu, saidai suna binta da kallon k'urullah, musammanma bak'uwar ta hajia babba. bayan kamar 4mnt hajia babba tace, ''aminiya kingantafa, ai zata iya nake gani?.
    Wani murmushin k'asaita hajia khaltum tasaki, tagyara zamanta tana k'arema Aysha kallo lungu da sak'o, Aminiya ai zancenma zata iya labarine, zan iya cemiki tunda muke business d'innan baki ta6a samun hajaba irin ta wannan lokacin, ai young girls irin wad'annan su ake so dama, ALLAH kad'ai yasan irin ribar daza'a samu anan 👉🏻🙎🏻‍♀tayi maganar tana nuna Aysha datayi k'asa dakai tamkar munafuka.
     Amma jikinta sai tsuma yakeyi saboda tsoro da firgicin zaurencen Nasu hajia babba, ko kad'an Aysha bata fahimtar komai a zancensu, saidai tanaji ajikinta ba alkairi baneba, addu'oin Neman tsari tafara a can k'asan zuciyarta......
     Hajia khaltume takatseta da fad'in yarinya yasunanki?.
      Muryarta Na rawa tace Aysha.

    Nice name!.

Cewar hajia khaltume. Daga nan suka sallami Aysha tatafi.
  
      Tana tafiya 6angarensu tana sharar kwalla, haka kawai taji tana tausayin kanta, gashi su hajia babba sun gargad'eta kada tasanarma kowa kiran dasukai mata, inba hakaba komi yabiyo baya ita tajama kanta.
    Gaff taci karo da Abu, dasauri tad'ago  kanta, amma kafin tasan wata bige ansauke mata Marika har biyu.
    Dafe kuncinta tayi saboda azaba, ke Dan ubanki bak'ya ganine?....
     Maganar matashiyar Husnah ta katseta.
    Dan ALLAH kiyi hak'uri Anty Husnah wlhy bankula baneba, Aysha tayi maganar tana durk'usawa ak'asa, haryanzu hannunta Na dafe a kuncinta.
       Muhseen yak'araso inda suke da sauri, yace k Husnah lfy kuwa?.
       Cikin huci tace wai 'Yar iskar yarinyarnan hartakai ta bangajeni, Muhseen.
     kiyi hak'uri to, tayi kuskure amma bazata sakeba, ke Aysha bata hak'uri.
     Hak'uri Aysha takuma bata cikin kuka.
    Hasnah taja tsaki sannan tara6a gefen Aysha tashige, harda takama Aysha yatsun kafa.
      Aysha tafashe da sabon kuka dantaji zafin takawar. shikansa Muhseen yaga takawar da Husnah tama Aysha, danhaka ya rintse idanunsa yayinda Aysha tafashe da sabon kukan, tabashi tausayi sosai, yace kiyi hak'uri kinji, watarana sai labari, idan kina tafiya kiringa kula.
     Aysha ta jinjina kanta tana share hawaye, sannan tamik'e.
       Lafiya kuwa ya Muhseen?.
     Kallonsa yayi yace babu komai Hafeez, Husnah Ce tamari Aisha wai ta bangajeta, shine nake lallashin ayshar.
       Itadai kawai zalincinta yamotsa, Dan nasan babu yanda za'ayi Yarinyar ta bangajeta tana sane, ALLAH ya sakamata.
    Ameen dai Hafeez.

Yinin yau zumbur Aysha ad'aki tayisa, kowa ya tambayeta saitace batada lafiyane, itakam sokawai take tasamu hanyar guduwa daga gidan, Dan bazata zauna acutar da'itaba.
    Babban tashin hankalintama shine gwaggo bintu, kokad'an bata cika damuwa da lamarintaba yanzu, yau d'innanma kowa yazo yaji damuwarta amma banda ita, takuma fashewa da kuka mai ban tausayi, lallai tayarda maraici daban yake, Inda mahaifinsu Nada rai waya Isa yamusu koda kallon kaskanci, tatuna gidansu da rayuwa irinta family nata....
    Haka taita kuka mai tsuma rai, hardai zazza6in gaskiya yasaukar mata.

Bishirah ce taita kula da'ita har zazza6in yasauka, koda tatashi da safe taji sauk'i sosai, saidai damuwa da fargabar abindasu hajia babba suke kullama rayuwarta gashikuma takasa sanarma koda bishirah ne saboda tsoron gargad'in dasukai mata.

*_Bayan sati d'aya_*
              Zuwa yanzun Aysha tahak'ura da yunk'urin guduwa, dantabi dukkanin hanyoyin daya dace amma babu nasara, yawan kula da ita da bishirah keyi kuma yasata sakin jikinta sosai, Dan bishirah tagirmi Aysha dakusan 2years.
              Yau tunda suka tashi suketa bautar girke-girke saboda zuwan ya khaleel k'asar, harma da Aunty zuwairah daga Lagos.
   Su Aunty Amatullah kuma sai gobe idan ALLAH ya kaimu.
       Zuwa k'arfe 2pm suka kammala komai, gidan yad'auki k'amshin girki dana turare, mafi yawan yaran gidan basu dawoba, wasu nawajen aiki, wasukuma basu dawo school ba.
     Suma su Aysha 6angarensu suka dawo sukai wanka.
      Wajen k'arfe uku Aunty zuwairah ta iso daga Lagos, yaran gidan basuwani damu da zuwantaba, saboda itama masifaffiyace kamar hajia babba, indai tazo gidan saita addabi kowa, k'annentane kawai suketa farinciki saikuma hajia babba.
    Sudai su Aysha tunda suka gama shigarmata da kayanta ciki sukadawo harabar gidan suka zauna, karatun littafin *magana jarice* Aysha ke karanta musu itada bishirah, Dan bishirah batayi karatun bokoba ita. lokacin sallar la'asar nayi suka shiga ciki, bayan sun idar suka kuma dawowa wajen suka zauna, zamansu baifi da 10minutes ba d'an gwari ya wangale k'aton bak'in gate d'in gidan.
   Jibga jibgan motocine bak'ak'e wulik keshigowa ajere harsu biyar.
   Da sauri Bishirah tamik'e tana fad'in ya khaleel ya iso. Haka kawai Aysha tasamu kanta da fad'uwar gaba, innalillahi... Tashiga ambata, mutan gidan duksun fito harda aunty Mamie.
   Saidai mutanen sauran motocin hud'u suka gama fitowa wad'anda ke sanye cikin bak'ak'en suit wulik sannan d'aya daga ciki yabud'e motar tsakkiya wadda tafi kowacce mota k'yau da tsari.
    Bak'ak'en takalma sau ciki masu matuk'ar k'yaune suka fara bayyana, saikuma farar k'afar wandonsa.
       Fitowarsa gaba d'aya tasaka Aysha ambatar masha ALLAH!! batareda tashirya fad'an hakanba.
    Dogone sosai kuma k'ak'k'arfa, dukda yanacikin suit farare hakan baihana cikar haibarsa bayyanaba, yanada haske sosai amma baza'a kirasa fariba kuma ba bak'i baneba, yana matuk'ar kama da mahaifinsu Alhaji Abdallah, saidai kawai yafishi fari, kamar yanda dukkan sauran yaran suka fishi haske, shida Tasleem ne kawai kalarsu d'aya, sunmmafi kama da juna.
     A 6angaren k'yawun fuska kam dolene kakirashi kamilalle, komai nashi masha ALLAH, a kwai hanci kam daidai da tsarin faffad'ar fuskarsa, gawani saje daya k'awata taswurar kamilalliyar fuskar tasa, bai tara sumaba kuma kansa ba kwal-kwal yakeba, yabar 'Yar kad'an data kwanta luf akan nasa tamkar mai sabon aski.
   Agaskiya guy d'in yahad'u masu karatu, tako ina ubangiji yayimasa k'yak'yk'yawar hallitta Dan bashida makusa, idanunsa kawai abin sone ga kowacce mace, Dan gsky ba maza dukaba keda girman ido da haske irinna *Ibraheem Abdallah Rufa'ee (J!)*
     Cikin takun k'asaitarsa yake nufo family nasa, saidai fuskarnan tasafa babu fara'a, amma kamala da dattako sun lullu6eta. Ammah ce tak'araso ta rungumeshi dafad'in oyoyo maigidana.
    Yafita tsawo sosai, yarik'eta da k'yau yanamai farincikin ganin kakar tasu, suma yaran suka k'araso gareshi sunamai farinciki damasa sannu dazuwa.
      Zame jikinsa yayi yak'arasa inda momy take itama ya rungumeta, my lovely son Sannu dazuwa.
   Yauwa momyna I miss you, yafad'a yana d'agowa daga jikinta, hannunsa takama tana dariya, nima haka yarona ina kewarka kusadani.
   Lallausan murmushinsa yasaki, sannan yanufi aunty Mamie dake tsaye itama tana murmushi.
     Hark'asa ya duk'a  yace Aunty barka da gida, munsameku lfy?.
    Hannunta takai tashafa kansa, idanunta cikeda hawaye saboda tuni Rufa'ee ta datayi, tace lfy lau babana, kunzo lfy?.
    Jinjina kansa yayi kawai, danta Sosa masa inda kemasa k'aik'ayi, tatuna masa d'an uwansa Wanda suka tashi tamkar tagwaye, komai nasu tare sukeyi, aikine kawai ya banbantasu, yamik'e jiki asanyaye suka k'arasa ainahin falon gidan.........🖊




CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now