33

3.4K 314 1
                                    

3⃣3⃣

           Kwanan sa kusan uku kenan da dawowa k'asar amma baije gidaba, saboda wani aiki daya rik'eshi, wani mutumi sukesan kamawa, kuma yanada had'arin gaske, kasancewar sa tsohon d'an ta'adda.
      Sun d'ana masa tarko sosai tun wajen wata 5 daya wuce, har yanzu ALLAH baisa ya fad'a a tarkonba.
     Mutumin a Rivers state yake, cikin port-harcourt.
        Cikin shirin Uniform d'in police interpol yake, yaukam da bindugu biyu yafito, kokad'an fuskarnan babu alamar sassauci, duk lokacin da ya khaleel yad'ora hular aikinsa yakan k'ara kwarjini da cikar haiba👮🏼‍♂.
    Sosai Uniform kemasa k'yau, gashi dogo mai suffar k'arfi masha ALLAH, cikakken training daya yasamu yakansaka suffarsa tsorata mazanma ba mataba kawai, ga tsare gida irinnan jaruman ma'aikata nagartattu.
          Cikin Nutsuwa yake tafiya, wadda hakan tamkar halittarsace, komai ya khaleel zai maka anutsuwarsa yake, komai zafin daya d'auka awajen aiki ko rikiCewar abubuwa kuwa.
    Bayansa Joseph ne da Youseef, Samuel, Adams, Taheer, saikuma mutum uku wad'anda bansansuba kam, da alama dai cikin k'ananun ma'aikatan suke.
    Da sauri d'aya aciki yabud'e masa motar, harya taka zai shiga saikuma yajuyo yana kallonsu, in serious tone yace, ''komai zakuyi kuyi da kula, saboda anguwar tanada jama'a, banason aikinmu yashafi wani mara laifi, so Ku kula.
      Kowa zaiyi tafiyarsa shi kad'aine, Adams shiga muje.
      OK sir!!! Suka fad'a tareda Salutes nasa.
      Batareda maida murtaniba yashige motar ya zauna abaya, yayinda Adams & Emanuel ke a gaba.
                 Kwantar da kansa yayi jikin kujera ya lumshe idanu, addu'oin Neman nasara ga ubangiji kawai yakeyi, yayinda gefen zuciyarsa take masa hasashen idan ta kwa6e ko ansami nasara.

Daka gansa kaga tibiran mahaukaci, kokad'an babu wata hujja dakakeda ita wadda zaka nuna rauninsa da amsa sunan mahaukacin, zaune yake kusada wani mai shayi Wanda yakasance ba haushe d'an balaguro, gefe d'aya kuma mai gasa naman tsirene da balangu, dandazon matasane awajen anata hirar duniya, wasu ta siyasa wasukuma ta yanayin rayuwa, harma da masu ta ball.
      Wani matashin saurayi dayaci indome yarage yamik'e zuwa gaban mahaukaci daketa zane-zane ak'asa, kaikace lissafin kud'i yakeyi kona shekarunsa.
     Mik'a masa filet d'in yayi, babu musu ya kar6a, saidai maimakon yaci, saiya juye cikin bak'ar ledan buhu datake hannunsa akowanne lokaci, yamik'ama matashin saurayi filet d'in yana tuntsura dariya.
    Girgiza kai kawai matashin saurayi yayi yakoma rumfar mai shayi ya zauna.
     Wani yace nifa kunsan wani Abu?.
    Akace a'a.
Tunda mahaukacin can yazo wajennan, kimanin watanni uku kenan, banta6a ganin yaci abinciba, komi zaka bashi saidai yazuba abuhun ledar can, kuma kullum anan yake kwana.
      Wlhy gaskiyanka ne, amma k'ila yanaci mune bama maida hankali shiyyasa bama ganewa.
      Wani yace, nifa tausayi yake bani, ruwan shekaran jiya duk akansa yak'are.
    Wlhy haka yakeyi, ammafa ni a kwanakin baya sonayi nad'an rud'e, sainaga mahaukacin daya fara zama awajennan tamkar yafi wancan d'in suffar k'arfi dad'an tsawo? Danni farkonma zuwansa ban yarda mahaukaci baneba.
      Ashe bani kad'ai nakula da hakanba, kasan ALLAH nima sainake ganin tamkar ba wannan baneba Wanda yafara zuwa, ni wannanma baifi sati 2 ba nafara ganinsa anand'in, saikuma na daina ganin wancan.
      Kudai kuna masa kallon tsorone, k'iladai aljanunsa ke canjashi, wani matashin saurayi ne mai wannan maganar, tun d'azu kuma baisaka baki a hirarba sai yanzu, yanata danna waya abinsa.

Jin shigowar sak'o yasaka ya khaleel bud'e shanyayyun idanunsa, wayar yad'auka yaduba, cikin d'an rikita yace, "Adams akwai matsala kenan?".
     Da sauri Adams yace sir! Matsalarmi kuma? Naga komai yana tafiya yanda muka tsarashi.
    Hakane, amma wai mutanen wajen sun fara tantama akan Mahfouz, yanzu katura masa sak'o yabar wajen, yaje inda muke had'uwa zanzo na samesa.
    OK sir!, Adams yafad'a yana k'ok'arin tura sak'o da wayarsa.

Sunata hirar mahaukaci, Wanda ko alamar yasan misuke fad'a baiyiba, kamar an tsikaresa sukaga yatashi yana lalube-lalube abuhunsa, barin wajen yayi yanata surutai kamar yanda yasaba, babu Wanda yadamu dabarinsa wajen, harya 6acema ganinsu.

CIKI DA GASKIYA......!!حيث تعيش القصص. اكتشف الآن