52

4.5K 335 0
                                    

  52

    Yana fita Aysha tasauke ajiyar zuciya, hijjabin jikinta tacire tayi simple kwalliya, tasaka siket da riga Na atanfa, kayan sunmata k'yau sosai, amma ita kokad'an bawani tadamu da sawar baneba, saboda gargad'in da mama tamatane kawai take kiyayewa.
     d'akinta tagyara tsaf, tasaka turare sannan tanufi falo shimadai gyaran kad'an tamasa tasaka turaren, tayi mamakin rashin ganin kayan abincin jiya, aranta tace, "k'ila ya khaleel ne yad'auke".
        Harta nufi hanyar kicin taji ana Knock d'in k'ofa, tajuyo dabaya danufin dubawa ya khaleel yashigo da sallama, Aysha ta amsa kanta ak'asa.
        d'an nesa da ita yatsaya, idonsa kyam akanta, saidai fuskar haryanzu babu walwala. yace, "tarenake da bak'i, kinzo kin tsayamin akai, kije kisaka hijjab zasu shigo".
      Haushine ya kama Aysha, batasan ta murgud'a masa bakibama, tawuce tana k'unk'uni batareda yaji mitake cewaba, ransane yad'an sosu, amma saiya danne yayimusu iso zuwa ciki, Dama suna bakin k'ofane tsaye.
             Masifa natacin Aysha a zuciya tana d'akko hijjab a wardrob tana tsogumin yanda halayen ya khaleel yake, shidai bazai ta6a kuyi magana mai dad'iba dashi, to yaushema yasakema mutane fuska, itafa gaskiya bazata iya wannan rayuwarba.....
         Tajiyo bayan tad'akko hijjab d'in danufin rufe wardrobe d'in taji tabuge Abu, ad'an figice tawaigo dansan ganin minene?. Bak'aramar fad'uwa gabanta yayiba ganin ya khaleel tsaye abayanta, kokad'an bataji alamar shigowarsaba.
       "Zan.....zan wu wuce".
    Tayi maganar cikin in ina da rawar baki, jikinta sai tsuma yakeyi.
    Bai motsaba, kuma bai tanka mataba, fuskarnan babu alamar sauk'i.
     Hakan yak'ara saka Aysha cikin tsoro, tatura murfin wardrobe d'in tareda jingina ajiki, idanunta Na kallon k'asa tana k'arema yatsun k'afafunsa kallo. Yayinda shikuma itad'in yake k'arema kallo, baita6a damuwa da kallon ya Aysha takeba a can baya, amma ayanzu saiya samu kansa dabin halittar jikinta da kallo daki-daki.
        Kad'an tad'ago ido ta kalleshi, ganin kallon k'urillar dayake matane tayi saurin saka hijjab d'inta. 
       Yalumshe manyan idanunsa yana kauda kansa, Aysha tara6a ta gefensa zata wuce cikin d'ari-d'ari.
     Da sauri yaruk'o hannunta, cikin Aysha yabada k'ululu!..
         "dawo magana zamuyi".
       Jiki a sanyaye tadawo baya, kafin yace wani Abu wayarsa tafara ring.
     Cirota yayi yaduba, taheer ne, batareda yad'agaba yasaki hannun Aysha yanufi k'ofa, saida yabud'e sannan yace, "kizo Ku gaisa, zasu tafine, sannan kitanaji bayanin dazaki Kare kanki akan murgud'amin Baki dakikayi". 'Baijira cewartaba yafice abinsa'.
     Bak'aramin rud'u Aysha tashigaba, itama tasan hakan ba daidai baneba, amma wlhy rantane bayason dizgin dayake mata.
       Jiki a sanyaye tabi bayansa, gudun karta k'ara wani laifin.
         Sannu da zuwa tamusu tanufi kichin, sukuma suna tsokanar ya khaleel d'in, wai daga kira yayi bulum ad'aki, miyakeyi?.
       Tsaki yayi yana hararsu, yaxauna a kujera yana ''fad'in duk abinda zuciyarku tabaku shi Ibraheem khaleel yakeyi".
    Dariya sosai suka Sanya masa da shak'iyanci irinnan abokai. Ayaha tafito daga kichin d'aukeda babban tire dake cikeda drinks, ta ajiye a tsakkiyar falon takoma, babu dad'ewa tadawo da snacks, ta ajiye takoma tad'akko glass cups, duk suka mata sannu.
     Cikin kunya take amsawa, anutse  tagaishesu, duk sun yaba da ayshan, harsuna taya abokinsu burna azukatansu, sunta tsokanarta irinnan abokan miji, bata iya cewa komai saidai murmushi.
    Ya khaleel kam saima karantse baya falon, waya yaketa dannawa batareda saka bakinsa a zancensuba.
      Aysha tamik'e tabar musu falon dansu d'an ci abinda ta ajiye musu.
      Shigarta d'akinta da y'an mintuna saiga anty glo...da kubrah, saida suka gaisa dasu ya khaleel afalo sannan suka shigo, bisa umarnin ya khaleel d'in.
    Zumbur Aysha tamik'e daga bakin gadon, Dan batayi zaton ganinsuba.
       Anty glo tashek'e da dariya tana "fad'in sholy amarsun ango, Ashe dama tsoron john Na k'aryane kikeyi, koda yake naga kinzama y'ammata, ina Antyan taki meerah?".
       Amamakinsu sai sukaga Aysha tayi murmushi, takoma bakin gadon ta zauna tana musu wani kallon rainin hankali, "mtsowww! Wlhy ku kama kanku, kenaga kanki rawa yakeyi glory!, inaga dai k'awar taki bata sanar dake wanene mijin nawaba ko? Karfa wajen tone tonen kaza, tatono wuk'ar yanka kanta".
       Kubra tabud'e baki zatayi magana kenan ya khaleel yaturo k'ofar ya shigo, kallo yabisu dashi su duka, glory da kubrah sund'anji shock da shigowar tasa, Aysha kam ko'a kwalar rigarta, Dan zuwa yanzu batak'i komai ya 6aciba.
         Ko kallo su kubra basu isheshiba, yace, ''taso kuyi sallama zasu tafi".
     Aysha tamik'e itama batareda ta kalli su kubra d'inba tanufi k'ofa.
    Ganin haka suma dole sukabi bayanta, bak'aramin Sosa ransu lamarin yayiba, suna mamkin yaushe Ayshan tawaye har haka? Lallai hajia laura kallon baibai takema Aysha, kuma dolene sud'auki mataki akan Aysha da meerah, Dan zasu 6allo musu ruwane.

CIKI DA GASKIYA......!!Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang