59

4.7K 322 2
                                    

59

       Tsorone yakuma kama Aysha, dan ganin ya khaleel na Neman kauce hanya, tarik'e hannunsa dake yawo ajikinta, tsayawa yayi cak yadaina kissing d'inta, jin yadaina tafara k'ok'arin zame jikinta daga nasa.
     Bai hanataba yabata dama tatashi zaune.
       Kwanciyarsa ya gyara zuwa rigingine, yay filo da hannunsa yana kallonta ta k'asan ido, sotake tatafi wanka amma tanajin tsoron tafiya yad'auki wayar, ita duk zatonta yagantane.
      Hijjab tad'auka tasaka, yad'an ta6e baki yana tashi daga kwancen dayake.
      Gyara zamansa yayi sosai yana kallonta, itakam kanta Na k'asa takasa kallonsa.
     "Ukkhhmm! Yay gyaran murya".
    d'ago idanu Aysha tayi tana kallonsa, yad'age girarsa d'aya yana wani yatsina fuska.
     Dariya yabama Aysha, Dan haka ta murmusa, shikuma yata6e baki yana jingina da gadon sosai.
          "zoki zauna muyi mugana". 'Yay maganar batareda ya kalletaba'.
     Bak'aramin fad'uwa gaban Aysha yayiba, tunaninta akan wayarne, haka tatafi jiki a sanyaye tazauna bakin gadon nesa dashi.
            Jawota yayi tadawo saman gadon sosai, yad'ora kanta bisa cinyarsa, "miyasa kika kasa sakin jikine dani har yanzun?, nifa sonake mu shinfid'a k'yak'yk'yawar rayuwar aure, A'eesha aure hak'urine kawai acikinsa, bakomaine ake nema asamuba, duk abinda akace masa ibadane to tabbas yanada wahala, banmiki alk'awarin farinciki 100% ba a aurenmu, Dan zomu zauna zomu sa6a, ballantana mutum Irina da ayyuka sukama yawa, inafata zakiyi hak'uri dani lokacin sa6ani da lokacin farinciki, insha ALLAH zan kula dake iya iyawata, nima nabaki dukkan amanata, kirik'emin, Dan kece sirrina ayanzun".
          Dad'i, farinciki, murna, duksun taru sun dabaibaye zuciyar Aysha, tarasa yanda zata musalta mitakeji, saidai Abu d'ayane ke ta6a zuciyar Aysha tawani 6angaren, har yanzu ya khaleel bai furata kalmar yana sontaba, shin kodai baya sontane? Itace keta shirmentane?".
      Ganin tayi shiru yad'an girgiza k'afarsa, da sauri ta kalleshi, saikuma ta kauda kanta ganin yakafeta da idanu.
       Lallausan hannunsa yasaka yamaido fuskarta, saita lumshe ido.
      "Bud'e ido ki kallenimana, nifa sonake kisaki jiki dani, banason wannan nuk'u-nuk'u d'in, saikace wata matar k'auye, banson shariya, kice wani Abu".
       Hannu tadaka tarufe fuskarta, "ALLAH inajin kunya".
      bakinsa ya ta6e, yace, "kunya kuma aii tak'are A'eesha, tunda kinbiya kazar dakikaci bashi, kinzama Ibraheem, Ibraheem yazama A'eesha", yay maganar yana janye hannunta, tareda sunkuyowa ya sumbaci goshinta.
         Dad'i Yakama Aysha, amma tanason ya khaleel yafurata mata kalmarso da bakinsa, dukda tagani a aikace bata gamsuba gaskiya, amma abinda talura dashi jin Kansa bazai bari yace yana sontaba, zatabishi su tafi ahaka itama.
           K'ok'arin cire hijjab d'inta yafarayi, ta kallesa da dasauri zatayi magana, amma saitaga ya had'e fuska, dole tahak'ura yacire, hannunsa yad'ora saman cikinta, d'ayan kuma yana shafa kwantaccen gashin goshinta, muryarsa a tausashe yace, ''ina binki bashin maganar danayi, Duke kin wani maidani aku, kekuma kinyi tsit, nifa ustazancinki mamaki yake bani".
            Ganin kamar da damuwa yake magana saita daure tace, "insha ALLAH zaka sameni mai biyayya agareka, saidai kayi hak'uri da dukkan kurakuraina idan nayi, koda kuskure, ko akan Sani saboda ajizancin Dan adam".
     "Hummm". kawai yace, yasauka daga gadon yafita.
    Da kallo tabisa haryakai k'ofa yajuyo yana kallonta, kiyi wankan zanje cikin gida Na gaisa dasu momy..  
     Kanta ta jinjina masa, ya ida ficewa.
     Da Sauri taduk'a k'asan gadonta tad'auki wayar harta d'an tsage, kashewa tayi tatura can k'asan kayanta acikin wadrobe, sannan tashiga wanka.

         _____________________________

           Saida yafara shiga 6angaren baffah suka gaisa, sund'an dad'e suna tattaunawa, baffah yace, "yaushe matarka zata koma wajen aikintane? Banason asamu matsala, kagadai kusan watanni 6 kenan tana k'ok'ari, watanni 6 kawai yarage mata ta mammala NYSC d'inta, baikamata aimata wasa da damartaba".
    "Insha ALLAH baffah zata koma ranar Monday insha ALLAH, nima ranar zan koma aiiki".
      " to shikenan ALLAH ya kaimu lfy".
    "Ameen".

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now