19

3.5K 279 0
                                    

1⃣9⃣

     Jikin Aysha har rawa yakeyi wajen dannama k'ofar key tana kuka dakiran sunan ALLAH, wata tsanar hajia babba da hajia kaltume da Na ratsata, cikin kuka tace, "gwaggo bintu kinci amanar zuminci, kinci amar ALLAH, kinci amanar maraici, ya ALLAH karka basu damar ketamin haddi, ya ubangijina badan niba badan halina katsareni daga sharrinsu, wayyo ALLAH na, ALLAH katsareni daga k'addarar zina, ina tawassali da sunayenka k'yawawa, dan alfarmar manzon nan namu mafi soyuwa agareka aduk cikin bayinaka, ya rabbi indai har dominka nakeson tsare kaina kakareni, bazayiba ya ALLAH..............
      Duk maganganun da Aysha keyi akunnen John dasu Anty glory ne, babu maijinta Dan dukansu basajin hausar, garama aunty glory najin kad'an, itama zaman turai yasata mata abubuwa dayawa a hausar.
     Jin yanda take fidda kuka duksai tausayinta yakamasu. Harshi kansa john d'in, haka kawai yaji bazai iya mata doleba.
    Ahanakali yashiga Knocking k'ofar yana fad'in babie please bud'e k'ofar, bazan ta6a ta6akiba saida izininki, kibud'e zanyi magana dakene, bazan cutar dakeba.
   Duk cikin harshen turanci yake maganar, bakowane kalma ayshan ke fahimtaba, amma tafuskanci Inda zancensa yadosa, saidai zuciyarta bazata ta6a aminta dashiba, domin hakan bai cancanta dashiba. Tazame jikin k'ofar tazauna jagwaf tana kuma sakin kuka mai tsuma zuciya dakiran sunan mama da Umma, tak'arashe dafad'in ALLAH ka k'u6tar dani daga zalincinsu.
   Shiru duk sukayi suna saurarenta dukda basajinta.
    Meerah kuma tamaki tamotsa daga inda take zaune, tanacan sai zabga kuka takeyi da tausayin halin da Aysha Zata tsinci kanta ayau.
    Amma jin abinda yake faruwa saita d'ago kai tana kallonsu tsaye cirko-cirko ak'ofar d'akinta, wannan yatabbatar mata cewa Aysha tasamu damar kulle kanta.
    Batasan sanda tasaki sassanyar ajiyar zuciyaba, ahankali tace, ''Alhmdllh ya ubangijin talikai.
      
Suduka suka bar jikin k'ofar, su happy sukadawo falon suka zauna, Anty glory da john kuma suka nufi d'akin Anty glory d'in, da'alama magana zasuyi.

              Bayan kamar mintuna talatin Anty glory tafito daga d'akinta, 'yanmatan takebi da kallo d'aya bayan d'aya, wannan ya tabbatar musu da john ya hak'ura da Aysha yana buk'atar d'aya acikinsune, kallon Anty glory yatsaya akan meerah, wannan yasa meerah tayi kivin-kicin da fuska, Dan damacan tatsani John, shine mutum nafarko daya fara keta mata haddi, kai gadukkan 'yanmatan ma, har wad'anda suka bar gidan ayanzun.
       Kamar Anty glory zatayi magana saikuma tayi shiru tamaida kallonta kan besi dasuka shigo ana rikicin Aysha.
     Besi oya tashi muje.
   Babu musu besi tatshi suka doshi d'akin Anty glory.

Aysha kam k'in bud'e kanta tayi har kusan bayan awoyi 6, saida meerah Tamata magana da kanta, takuma tabbatar mata da john yabar gidanma tareda rantse mata sannan tabud'e d'akin..............

__________________________
     Tun Bishirah nazuba idon ganin dawowar Aysha kusa harta fidda rai, Dan babu Aysha babu gwaggo bintu.
   Lamarin yafara damun bishirah hartama iya hama magana akan hakane.
   Itakamta iya hama lamarin yad'aure matakai, Dan gwaggo bintu bata ta6a tafiya Kano tadad'e hakaba.
    Randa su Aysha suka cika sati biyu da Barin k'asar gwaggo bintu tadawo gidan Alhaji Abdallah, saidai babu Aysha, tambayakam tashata harta fitar hakali, daidai da musleem kasa hak'uri yayi saida yatambayi gwaggo bintu, danshifa tun randa yaga Aysha yakamu Da son yarinyar, yakuma yima Kansa tanaji da kamu, Wanda baisan yayi (abanzaba), gabad'aya gwaggo bintu sotayi tarud'e lokacin dataji musleem yace tabasa address d'in gidansu Aysha a Kano, zaije dakansa yadawo da'ita, shida kud'insama zai sakata makarantar.
    Cikin in'ina da had'iyar mugun yawu tace um...um alhaji k'arami kabarmusu 'yarsu kawai, Nima saida sukaci muntuncina suka kwace abarsu, to...to aganina barar musu ita yafi komai alfanu da zaman lfy....
   Yanda take zufa babu gaira babu dalili yasaka musleem tsura mata idanu.
    Shikansa ya khaleel dake kan dining yana lunch saida yad'ago ido yana kallonta, (kunsandai ma'aikaci, kuma irinsu ya khaleel da bincike yazamemusu jiki, koyaya rashin gaskiya yake tattare dakai saisun haskoka).
    Baiyi niyyar saka baki amaganar tasuba, amma yanda yaga gwaggo bintu nazufa dukda sanyin AC dake falon saiya kafeta da manyan idanunsa masu rikita Mara gaskiya.
      Cikin muryarnan tasa mai karsashi yace Maman yara kibasa mana, idanke sunmiki shibazasu masaba aii, idanma damatsala sai Anty mamie taje dakanta, dannaji itama tanada burin maida yarinyar school.
     Bak'aramin tsorone yabayyana ga gwaggo bintu ba, Dan hard'an guntun fitsari tasaki azanenta, tunda take da khaleel agidan basu ta6a magana mai tsawo kamar hakaba, saboda shi ba mutum bane maison yawan magana ballema hartayi tsawo atsakaninku, kumama bayashiga harkar kowa agidan, baya saka 'yan aikin gidan wani aiki, kome yakeso amasa saidai yafad'ama Anty Mamie  ko momy susakasu su masa.
     Idonsa yakauda akanta, yamaida kan filet d'in albus d'insa, kusan mintuna 2 bai d'agoba, su gwaggo bintu ma duksunyi shiru daga ita har musleem dake murnar shigar ya khaleel azancen.
    Yakuma kafe gwaggo bintu da  idanunsa, haka kawai yad'ora alamomin tambaya (??)akan matar, kauda idonsa yakumayi akanta yamaida kan musleem dashima yakafeta da idanu.
     Kai! Kabarta tunda tagaya maka reason nata, why not kahak'ura tunda bakasan sirrin families nataba.
       Kamar musleem zaifasa ihu yagyad'a kai, Dan tarbiyyarsuce bin maganar magana dasu.
    Ya khaleel baikuma cewa komaiba yacigaba dacin abincinsa hankali kwance.
                     Kowa afalon yayi mamakin saka bakinsa dayayi amaganar, Dan sunsansa baya shiga abinda baidameshiba, haka yake tun yana yaro.
      Ammah dakecan gefe zaune tace dadai tabayard'in sai a kar6ota, Dan yarinyar tanada hankali, ni wlhy kamama takemin da fad'ima tunda nafara ganinta.
    Aunty Mamie tace, "Amman ashe bani kad'aiba Na hango kamarnan, wlhy tunranda Maman yara tazo da yarinyar naga kamarsu da Yaya fad'ima.
           Gwaggo bintu dai bata fahimci maganar tasuba, ita tama k'agara tabar falon.
       Muhseen yace, "wace fad'imar?".
        Matar babankuce, amma sun rabu tun bayan haihuwar iro da wata uku.
     Shiru kowa yayi Afalon, Amal dake kiyama su nuri aikin islamiyya tace nikam ina kwad'ayin ganinta wlhy.
    Ya khaleel daya kammala cin abincinsa yamik'e yabar falon batareda yasake tankawaba.
     Kowa da kallo kawai yabisa.

_________________________
      Rayuwa tanata shurawa, kowace rana akwai abinda zai faru, wani farinciki wani abin kuka, wani Na al'ajabi, wani Na mamaki.

To zamu iyacewa zuwa yanzu Aysha tana cikin Na farincikin, saboda samun k'yak'yk'yawan labari datayi ga Anty glo....., kowa ya kalleta agidan yasan tana tareda farinciki.
       Ameerah dake kwance agadonta tana charts takai dubanta ga Aysha dake addu'a bayan ta idar da sallar dare data zame mata jiki akowacce rana.
           Jitai idonta yacika da kwallah, tashare da sauri saboda juyowar da Aysha tayi tana kallonta.
   Anty meerah wai yaudai babu inda zakuje kenan?.
     Murmushin yak'e meerah tayi, tatashi zaune tana tufk'e gashin dokin data k'arama kanta, my lil Sholy nicedai ban fitanba, amma su Queen aii tuni sun tsufa a club, yau hardama Anty glo....
       Ido Aysha tad'an zaro, Anty meerah da gaske? Dama Anty glo..... Tana zuwa club itama?.
              Wata 'Yar dariya meerah tasaki, kai lil sholy kinda abin dariya, aii tafiyar tamu duk d'ayace da ita, nima abinda yahanani fita saboda kene, banason abarki ke d'aya agidan. Waima mi aunty glo.....tafad'a miki jiya danaga takiraki d'akinta?.
        Mik'ewa Aysha tayi daga inda tayi sallan, tacire hijjabinta, doguwar rigace ajikinta pink har k'asa, tayi masifar mata k'au da haska farar fatarta, gashi tad'an k'ara girma da murjewa saboda yanayin k'asar ya kar6eta.
         Prigh tanufa tad'akko robar ice-cream, Zama tayi abakin gadon, tareda bud'ewa tafara shan kayanta, itadai meerah tana binta da kallo.
    Anty meerah waikinsan mita fad'amin?.
    Saikin fad'a lilyna.

Humm catayi wai mutumin ranar yace, "tamaidani school, yanzu haka sunkammala komai akan makarantar, zanfara zuwa, wai yanaso na iya turamci sosai.
     Waini Anty meerah waye shi agidannan?.
        Girgiza kai kawai meerah tayi cikin k'unar rai, tace, "Aysha bani Aron hankalinki nan nafad'a miki mikikazoyi  *Cayman islands (UK)*.
        Aciki zakiji tarihina da k'addarar data kawoni nan, dukda dai dagabaya muka dawo wannan k'asar, da a India muke zaune.

           Idon Aysha kam akan meerah dake sharar kwallah, itama duksai ranta ya jagule. amma tana saurarenta.
     Meerah race...........

Amin afuwa muhad'u page 20 danjin mi meerah zata sanarma ayshar ne🤔?????.

*************************
       Ya khaleel kam yaje k'asar Indonesia, inda yay kwanaki 9, dama aikine yakaishi, yabaro k'asar yanufi France inda Headquarter d'insu take, a birnin *Lyon*, nan d'inma yasamu kwanaki 12 yabaro yataho k'asar haihuwarsa Nigeria............🖊

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now