60

5K 330 1
                                    

60

          Aysha tabud'e k'ofar shikuma yakwaso ledojin daya ajiye suka shiga, afalo suka yada zango, yana ajiye ledojin yajuya zuwa masallaci, Aysha kuma tatafi d'akinta itama tayi sallar.
     Bai shigoba har Aysha tadawo falon, tazauna akan doguwar kujera tana danne-danne awaya dan babu wuta and'auke.
        Kusan mintuna 10 da zamanta aka kunna Gen...., haske ya gauraye ko ina, saiga ya khaleel shima yashigo, sannu da zuwa tamasa.
    Ya amsa babu yabo babu fallasa, d'akinsa yashiga, kusan mintuna 15 yafito d'aukeda laptop ahannu, yacire kayansa, yacanja zuwa 3quarter da best.
          Ya ajiye kayan hannunsa sannan ya zauna, Aysha tamik'e tad'akko masa ruwa.
         Zubawa tayi tabasa yasha, yamik'a mata kofin yana fad'in thanks.
     Jinjina kai kawai tayi batace komaiba.
      Ya kalli ledojin daya ajiye suna nan inda yabarsu, d'ago manyan idanunsa yayi yazubasu kan Aysha, fuskarsa ahad'e yace, "su wad'annan ledojin misukeyi anan?".
         "um..um....kayi hak'uri Dan ALLAH, Na mantane wlhy".
      Baice komaiba yaja k'aramin table Na glass yad'ora k'afafunsa akai, sannan yad'ora laptop d'insa daya d'akko bisa cinyarsa yasaka siririn farin glass.
      Laptop d'in ya kunna, yashiga aikinsa.
         Aysha tana kichin tana bud'e ledojin, kayan fruits ne sai gasassun kaji guda biyu da robar ice-cream guda biyu, saikuma fura guda uku.
     Komai d'aya tad'auka, tazuba sauran a fright tafito, tana ayyanawa azuciyarta yau komai zai faru bazataci kazar nanba, haka kawai yadawo yace tabiyashi kuma, har yanzun bata manta da wahalar data shaba adaren ranar, koda yake shima aiya gane kuransa tunda harya fita jigatama, kusan kwanaki 2 yana shan ciwo harda k'arin ruwa..

     Sosai hankalinsa nakan aikin dayakeyi, ta ajiye tiren kusadashi, ahankali tace, "bismillah".
          Batareda ya kalletaba yace, "zauna anan ki d'ora bisa cinyarki, yay maganar yana nuna mata gefensa, dayake akan doguwar kujera yake zaune.
        Bayanda zatayi dole ta zauna kamar yanda yace, yanzuma bai kalletaba yace, ''saiki ciyar dani, Aramawa kura aniyarta".
       Idanu Aysha tazaro waje, sannan tace, ''wayyo ya khaleel, nifa....nifa wlhy"....
        Juyowa yayi yana kallonta, saita kasa cigaba da maganar, yajanye idonsa yamaida kan laptop d'in, "ashe babu dad'i ke nake baki kici, oya maza kan aikinki, kuma banda k'atuwar lauma".
        "Nifa na k'oshi, tayi maganar a shagwa6e".
        Yata6e bakinsa, "hummm, kuma bazai hanani abinda nayi niyyaba ba, gwamma kicima kisan cikikayi kika biya".
        Dama abinda take gudu kenan, taci Kazan yace kuma saita biyashi kamar ranar.
    Jin tayi shiru yajuyo ya kalleta, dariya tabashi yanda tayi wani kwale-kwale da idanu, aransa yace, " sai tsiwa ga tsoro".            Afili kuma yace, ''infa tahuce yazama sau biyu kenan, kuma babu k'oraf.......".
      ......aibama tabari yakai k'arshen maganarba, tad'ibo Takawo bakinsa.....
         "Hhm, d'uran k'arfi zakimin?".
      "wlhy kaifa ya khaleel d'inan........
   Tayi shiru takasa k'arasawa.
          "Nifa ya khaleel me?, dukdai yanda kikai dani, haka zanyi dake agado, garama kibini a sannu ehe, kuma kidaina cemin wani ya khaleel, daga yau *_Sadauki!_* nakeso.
        Idon aysha yacika da kwallah, danjin wannan k'arfa-k'arfa, itadai addu'arta ALLAH yasa wasa yakeyi, ba irin abun shekaran jiya yake nufin mataba".
        Haka tacigaba dabashi naman abaki ahankali, shikuma yanata aikinsa a laptop hankali kwance, yayinda ak'asan zuciyarsa yakejin wani nishad'i da sarauta, yana lura da Aysha ko sau d'aya bataci namanba.
     Dariya yayi a zuciyarsa, yana tunanin dama akwai abinda zai tsoratar da Aysha haka harta iya danne kwad'ayinta? Dan yaga ko ice-cream bata kallaba, baice da ita k'alaba, har saida ya tabbatar ya k'oshi sannan yace, "Alhmdllh dainamin d'ura hakanan, karna kasa sunnah anjima".
    Ita bamata fahimci Inda zancensa ya dosaba, tamik'e zata maida kayan kichin yace, "dawo aii ba'a gamaba".
      Dawowatayi tazauna, duk tsoronsa ya gama kamata, mamakinma wad'annan abubuwan dayakeyi take ita.
      Kunsan Mintina 3 sannan ya ajiye laptop d'in gefe yajuyo sosai yana fuskantarta, tiren yakar6a yamaida kan cinyarsa fuskarsa k'unshe da murmushin mugunta yad'ebo naman yakai bakinta.
       ''ALLAH Na k'oshi ya k...... Amin Sadauki....ta canja maganar tata saboda uwar harara daya balla mata".
        "Kinga gwamma ma kici, Dan babu d'aga k'afa babu alfarma, Niba cazanyi kibiyaniba aii, da zuciya d'aya nabaki".
    d'ago idanunta tayi takallesa Dan tabbatar da gaskiyar maganarsa, ya jinjina mata kai yana lumshe idanu, dukda ba yandda tayi dashiba dai tabud'e bakinta ya  bata, haka yayta bata naman saida yaga taci da yawa sannan ya k'yaleta.
     Ruwan data kawo ya wanke hannunsa aciki, yad'auki cup yazuba fura, ita kuma yamik'a mata ice-cream yana fad'in nasan anan kikafi kauri".
        Da mamakin furicinsa tace, " kamar ya?".
    "Kamar yanda kika Sani, yay maganar batareda ya kalletaba, saima k'ok'arin canja tasha dayakeyi a TV, yamaida NTA domin  kallon labarai.
    Tunanin Aysha yafara canjawa akan ya khaleel, tafara Zargin anya kuwa baisan Wani abuba Dangane da  ita?.
        Ganin kallon datake masa yad'an juyo ya kalleta sannan yamaida hankalinsa kan TV, "yayadai kike kallona?, konayi wani abun mamakine?".
      "A'a Aysha tafad'a tana girgiza kanta a sanyaye, daga nan babu Wanda yasake tankawa, kowa da abinda yakeyi, yanashan fura yana kallon labarai, itama tanashan ice-ceam tana kallon labaran.
         Harsuka gama kallon labarai babu wata hira data kuma Shiga tsakaninsu, ya khaleel ya tattare kayansa waje d'aya, azatonta zai tashine yashiga d'aki, saitaga yazame ya kwantar da Kansa saman cinyarta.
    Aysha tazaro idanu waje, amma takasa yin magana.
     Shima bai tankaba, dukda yana kallon mamakinta ta gefen ido.
    Canja tashar yayi yamaida wisal Hausa TV , Tafseer akeyi, hankalinsa yamaida kan tvn.
    Itama Aysha saita maida hankalinta akan wa'azin.
   Sai kusan 11:30pm aka kammala tafseer d'in, ya khaleel yamik'e yana fad'in Alhmdllh, Malam mungode, ALLAH yabiyaku.
    Itadai Aysha batace komaiba, yakwashi kayansa yashige d'akinsa.
   Itama d'an kaye-kaye tayi tashige nata d'akin.
     Kowannensu yay shirin barci, hankalin Aysha kwance ta kwanta, tunda tasan ta kulle d'akinta, ko ya khaleel yayi yunk'urin shigowa babu dama.
      Takuma tura key d'in k'ark'ashin filo, sannan ta gyara kwanciya tanamai jin dad'in yima ya khaleel wayo.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now